0 Comments

Mutanen kauyen Katarko sun ce da damansu sun kwana cikin daji, bayan maharan Boko Haram sun kutsa cikin kauyensu tare da bude musu wuta.

Wani da ya shaida al’amarin ya ce mayakan ga alama sun batar da kama ne kuma suka shiga har cikin kauyen duk da sojojin da ke tsare shi.

Lamarin dai ya sa ala tilas sojojin da fararen hula suka tsere.

Wasu daga cikin mutanen kauyen sun samu mafaka a makwabtakan kauyuka, yayin da wasu suka tsere zuwa Damaturu, babban birnin jihar Yobe.

Shaidan ya fada wa  HausaPlus cewa ‘yan ta-da-kayar-bayan sun kuma kona mazaunin sojoji kuma har zuwa safiyar yau wata igwar soja na ci da wuta kafin shiga Katarko.

Babu bayani game da mutanen da aka kashe ko aka jikkata, sai dai bayanai na cewa an fasa shaguna a garin, abin ya sanya su zargin ko neman abinci da kayan masarufi ne ya kai maharan wannan kauyen.

A baya-bayan nan dai ana fuskantar karuwar hare-haren Boko Haram, inda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa ko a ranar Litinin, harin da ‘yan ta-da-kayar-baya suka kai a garin Kukawa cikin yankin tafkin Chadi ya janyo batan sojoji 16, bayan karawar da suka yi.

AFP din ta kuma ambato wani shafin intanet na kungiyar IS a Afirka Ta Yamma na ikirarin kai wannan hari, wanda a cikinsa ya ce sun kashe sojoji 15.

Maharan sun afka garin ne da yammcin jiya Laraba, inda suka bude wuta, lamarin da ya sa mutanen garin suka shiga daji.

Wani mutum da ya tsere cikin daji tare da iyalansa, ya shaida wa BBC cewa tun da misalin karfe 5 na yammacin jiya maharan suka fara harbin kan mai tsautsayi dalilin da ya sa suka gudu suka shiga daji.

Ya ce tare da jami’an tsaro suka gudu suka shiga daji a lokacin da maharan suke harbe-harbe.

“Mata da kananan yara sun firgita matuka inda suke cikin tashin hankalin rashin sanin abin da ke faruwa ga ‘yan uwa da ke cikin garin,” in ji shi.

Kawo yanzu ba a san ko akwai wadanda suka rasa rayukansu ko jikkata ba a harin.

Yobe na daga cikin jihohin yankin arewa maso gabashi da suka dade suna fama da hare haren Boko Haram.

Author

ilh5qdbyak81@n3plcpnl0159.prod.ams3.secureserver.net

Leave a Reply

Your email address will not be published.