0 Comments

A wani taron manema labarai da Alhaji Atiku Abubakar dan takarar jam’iyyar PDP ya gudanar a Abuja, ya bayyana cewa sakamakon babban zaben da aka bayyana ‘almara ce kawai’ kuma ba zai amince da shi ba.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi takarar shugabancin kasar ne a karkashin jam’iyyar PDP, inda ya sha kaye a hannun Shugaba mai-ci Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC.

Atiku ya ce “a matsayina na dan Najeriya ina ganin wannan zaben na zamba da INEC ta gudanar ba shi da ingancin da zai samar wa ‘yan Najeriya shugaban kasa domin ba ra’ayinsu kenan ba”.

Ya kuma bayyana dalilin rashin amincewa da sakamakon kan cewa kuri’un da Buhari ya samu a wasu bangarorin kasar sun wuce kima, ciki har da jihohin kudu maso kudu da kuma na Arewa maso gabas wadanda yakin Boko Haram ya daidaita.

“A jihar Akwa Ibom misali, an samu raguwar yawan rajistar masu zabe da kashi 62% daga zaben shekarar 2015, hatta a inda rajistar masu zaben da kuma wadanda suka karbi katin jefa kuri’a take da yawan gaske a zaben da ya gabata.

‘Wannan kuskuren an kuma maimaita shi a jihohin da PDP ke da karfi kamar Delta da Rivers da Abia da kuma Benue, inda a Borno kuma aka samu karin kashi 82% na rajistar masu zabe. Kai ka ce rashin tsaro kamar bai wa a gare su wurin yawan kuri’a”.

Bisa wannan dalilki ne kuma Atiku Abubakar ya ce ya yi watsi da sakamakon zaben tare da bayyana cewa har yanzu bai fitar da rai ba.

taswira

Atiku ya ce wannan zaben shi ne mafi muni da aka taba gudanarwa a Najeriya a cikin shekara 30.

“A shekara 30 da na yi a harkar siyasa wannan shi ne zabe mafi muni da na taba gani a Najeriya.

“Kuma na gaya wa Janar Abdussalami Abubakar lokacin da ya kira cewa hatta zabukan da gwamnatocin soja suka gudanar ya fi shi inganci.”

Presentational grey line

Yadda zaben yake?

Duk dan takarar da ya samu kuri’un da suka fi yawa, idan dai har ya samu kaso 25 na kuri’un da aka kada a jihohi 24 daga jihohi 36 na kasar.

‘Yan takara 73 ne suke neman kujerar shugabancin kasar amma fafatawar ta fi zafi tsakanin ‘yan takarar jam’iyyu biyu.

Taken Jam’iyyar shugaba mai ci, Muhammadu Buhari shi ne ‘Next Level’ wato kai Najeriya zuwa matakin ci gaba.

Ita kuma jam’iyyar adawa ta PDP wadda tsohon mataimakin shugaban kasar, Alhaji Atiku Abubakar yake takara na da taken ‘to get Nigeria working again’, abin da ke nufin jam’iyyar za ta dawo wa najeriyar hayyacinta.

Atiku Abubakar ya kalubalanci Shugaba Buhari da lalata shekaru hudun da ya kwashe a kan karaga.

Dukkanin ‘yan takarar guda biyu dai sun fito daga yankin arewacin kasar mai yawan musulmai. Kuma dukkanninsu sun wuce shekara 70 da haihuwa.

Matsalolin Najeriya

Najeriya ce dai kasa mafi girma a yawan jama’a da kuma yawan albarkatun man fetur. To sai dai rashawa da cin hanci da kuma gaza zuba rarar da ake samu daga sayar da man a kasuwar duniya ne ke tarnaki ga cigaban kasar.

A 2016, kasar ta samu komadar tattalin arziki. An kuma samu jan kafa kafin kasar ta samu ta farfado, al’amarin da ke nuni da cewa ba a samar da isassun ayyukan yi ga miliyoyin matasan kasar da ke neman aiki ba.

Za a iya cewa kaso daya bisa hudu na matasan kasar ba su da abun yi.

Alkaluman masu zabe

•Yan takarar shugaban kasa guda 73

•Masu katin zabe miliyan 84

•Kaso 51 da masu kati ‘yan kasa da shekara 35

•Akwai rumfunan zabe dubu 120a fadin kasar.

Presentational grey line

Shugaba Buhari ya ce ya murkushe kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin kasar, to sai dai har yanzu kungiyar na da karfi.

Sannan kuma ana ta yawan samun rikici tsakanin manoma da makiyaya a yankin arewa maso tsakiyar kasar.

Najeriya dai ta fuskanci mulkin soji har zuwa 1999, duk da cewa an samu gwamnatocin dimokradiyya wadanda ba su yi tsawon rai ba kafin nan.

A bana kasar ke cika shekara 20 da dawo wa turbar dimokradiyya.

A 2015 ne aka zabi shugaba Buhari, lokacin da kasar ta kafa tarihi, inda dan takarar jam’iyyar adawa ya kayar da shugaba mai ci.

Author

ilh5qdbyak81@n3plcpnl0159.prod.ams3.secureserver.net

Leave a Reply

Your email address will not be published.