0 Comments

Liverpool da dan wasanta Mohammed Salah na Masar mai shekara 27, sun yi watsi da tayin fam miliyan £150 na Real Madrid da Juventus kan dan wasan. (Mirror)

Dan wasan tsakiya na Manchester United Paul Pogba yana shirin zuwa yajin aiki domin matsin lamba kan bukatarsa ta komawa Real Madrid. (ABC – da sifaniyanci)

Ole Gunnar Solskjaer na dab da rasa dan wasan gaba na Atltico Madrid Antoine Griezmann, mai shekara 28, yayin da Barcelona ke shirin lale fam miliyan £150 domin mallakar dan wasan na Faransa. (Mirror)

Manchester United za ta karawa Marcus Rashford, mai shekara 21 albashi inda zai dinga karbar fam £350,000 a mako, domin janyo ra’ayinsa ya ci gaba da taka leda a Old Trafford a yayin da Barcelona da Real Madrid suka fara farautar dan wasan. (Sun)

Gabriel Jesus mai shekara 22 ya yi watsi da rahotannin da ke cewa da shi da Sergio Aguero mai shekara 31 za su bar Manchester City.(Mail)

Christian Benteke mai shekara 28, yana son ci gaba da murza leda a Crystal Palace duk da wasu rahotannin da suka alakanta shi da komawa China. (Standard)

Dan wasan Chelsea Tiemoue Bakayoko, mai shekara 24, ya ce wata rana yana son ya koma taka leda a Paris St-Germain. (L’Equipe – da Faransanci)

Arsenal za ta sake taya dan wasan Faransa Alexis Claude-Maurice karo na uku bayan samun fahimta juna tsakaninta da dan wasan mai shekara 21. (Metro)

Mako biyu ya rage kwangilar Rafa Benitez ta kawo karshe da Newcastle, amma kocin mai shekara 59 har yanzu ya ki amincewa ya tsawaita kwantaraginsa. (Newcastle Chronicle)

Author

ilh5qdbyak81@n3plcpnl0159.prod.ams3.secureserver.net

Leave a Reply

Your email address will not be published.