0 Comments

Babbar kotun kolin Najeriya ta ce jam’iyyar APC ba ta yi zabukan fitar da gwani ba, don haka jam’iyyar da take bin APC a yawan kuri’u ita ce ta lashe zabukan jihar da aka yi a watan Maris.

A zaman kotun na ranar Juma’a ta yanke hukuncin cewa jam’iyyar APC ba ta gudanar da sahihin zaben fidda gwani ba gabanin babban zaben shekarar 2019 a jihar.

Hukuncin kotun ya jaddada hukuncin da kotun daukaka kara a jihar Sokoto ta yanke, wadda ita ma ta yanke hukuncin cewa jam’iyyar APC ba ta gudanar da sahihin zaben fidda gwani ba a jihar.

Kotun kolin ta ce jam’iyyar ba ta da halaltattun ‘yan takara don haka ba za ta iya kasancewa wadda ta lashe zabukan jihar ba.

Hakan na nufin APC ta rasa kujerar gwamna da dukkanin kujerun ‘yan majalisar Tarayya da na jiha.

Tun farko dai Sanata Kabiru Marafa ne ya fara shigar da kara a gaban kotu, inda ya kalubalanci zaben fidda gwanin da APC ta yi.

Jam’iyyar adawa ta PDP a kasar ta wallafa hoton wanda ya yi mata takarar kujerar gwamna a karkashin jam’iyyar, Bello Matawallen Maradun inda ta ce dimokradiyya ta yi nasara.

Ra’ayoyin jama’a game da hukuncin kotun kolin daga shafin Twitter

Karin bayani game da Zamfara:

Tasawirar jihar Zamfara
 • Kashi 67.5 ke rayuwa cikin talauci
 • Iya karatu da rubutu: Kashi 54.7
 • Take: Noma tushen arzikinmu
 • Yawancin mutanen jihar manoma ne daga Hausa Fulani
 • Yawan jama’a: Miliyan hudu da rabi (Alkalumman shekarar 2016)
 • Musulmi ne mafi yawa
 • Jihar da aka fara kaddamar da Shari’a – a 2000
 • Madogara: Shafin alkalumma na Najeriya da wasu

Asalin rikicin APC a Zamfara

Gwamna Abdulaziz Yari da dan takararsa kwamishinansa na kudi, Alhaji Muktar Shehu IdrisHakkin mallakar hoto@MANCY4REAL
Image captionGwamna Abdulaziz Yari da dan takararsa kwamishinansa na kudi, Alhaji Muktar Shehu Idris

Jam’iyyar APC a jihar Zamfara ta rabu gida biyu ne, wato bangaren gwamnan jihar mai ci Abdul’aziz Yari da kuma daya bangaren na Mataimakinsa da ministan tsaro da Sanata Marafa da Hon Jaji.

APC a Zamfara ta gaza gudanar da dukkanin zaben fitar da ‘yan takararta na gwamna da na yan majalisar tarayya da na jiha.

Rikicin na APC a Zamfara ya samo asali ne bayan da Gwamna Abdulaziz Yari ya sanar da goyon bayansa ga kwamishinansa na kudi, Alhaji Muktar Shehu Idris, a matsayin wanda zai gaje shi.

Wannan ne ya sa wasu daga cikin masu sha’awar takarar gwamnan a jam’iyyar APC su takwas da suka hada da mataimakin gwamnan Ibrahim Wakalla da kuma Ministan tsaro Mansur Dan Ali suka hade kai domin yakar gwamnan na Zamfara.

Sau biyu ana shirya zaben fitar da gwanin a jihar, amma sai a soke saboda rikicin siyasa tsakanin bangarorin jam’iyyar a jihar.

Bangaren gwamnan jihar, ya fake ne da sakamakon wani hukuncin babbar kotun jihar a Gusau, inda alkalin kotun ya ce an yi zabe tare ba hukumar zaben kasar umurnin karbar sunayen ‘yan takarar bangaren gwamna da ya yi ikirarin gudanar da zaben.

Hukuncin wata babbar kotun tarayya a Abuja, ya tabbatar da matsayin hukumar zaben kasar na haramta wa duk ‘yan takarar jam’iyyar APC daga Zamfara shiga zabukan kasar da za a yi cikin watan gobe da na jibi.

Hukuncin ya ci karo da na kotun jihar karkashin mai shari’ah Muhammad Bello Shinkafi.

Sai dai mai shari’a Ijeoma Ojukwu ta kotun tarayya ta jaddada matsayin INEC inda ta ce jam’iyyun siyasa za su ci gaba da yin karan-tsaye ga ka’idojin zabe muddin suka kasa mutunta sharuddan da aka shata na jadawalin zabe.

Kotun ta ce hukuncin darasi ne ga sauran jami’yyun siyasa a nan gaba.

Bayan dage zaben 2019 ne wata kotu a Abuja ta ba hukumar zabe umurnin ta karbi ‘yan takarar jam’iyyar APC, matakin da ya sa APC ta shiga zabukan 2019 a Zamfara.

Wata kotun daukaka kara a Sokoto ce kuma ta soke hukuncin umurnin da kotun Abuja ta bayar, inda kuma bangaren gwamnati ya daukaka kara zuwa kotun koli.

Yanzu kuma Kotun koli ta soke zaben ‘yan takarar jam’iyyar APC.

Manyan ‘yan siyasar da hukuncin ya shafa

 • Abdulaziz Yari ya rasa kujerarsa ta sanata
 • Mataimakin gwamna Ibrahim Wakkala
 • Tsohon Minista Ikra Bilbis ya rasa kujerar sanata
 • Sanata Marafa ba zai koma majalisa ba
 • Tsohon gwamna Yariman Bakura siyasarsa ta uban gida ta kare

Author

ilh5qdbyak81@n3plcpnl0159.prod.ams3.secureserver.net

Leave a Reply

Your email address will not be published.