0 Comments

Masana harkokin shari’a a Najeriya na ci gaba da tofa albarkacinsu dangane da bijirewa umarnin wata babbar kotun da gwamnatin Kano ta yi bayan nadin sababbin sarakuna hudu a jihar.

Wata lauya mai zaman kanta a jihar, Barrista Maryam Abubakar ta ce la’akari da abubuwan da suka faru a baya, bijirewa umarnin kotu ba wani sabon abu ba ne.

Ta ce a baya an sha bayar da irin wannan umarni har a gwamnatin tarayya amma sai ka ga an bijire, sai dai hanzarin da gwamnati ta bayar shi ne ita ba ta karbi kowane umarni daga kotun ba.

Amma lauyar ta ce duk da cewa gwamnati ta bayar da nata uzurin da ta fake a kai, wadanda suka shigar da karar na da damar su sake shigar da cewa lallai an karya umarnin kotu.

Kalaman lauyar na zuwa ne bayan gwamnatin Kanon ta mika wa sabbin sarakunan masarautu hudu da ta kirkira sandunan girma.

Gwamnatin dai ta yi gaban kanta duk kuwa da umurnin da wata babbar kotu ta bayar cewar ta dakatar da duk wata harkar da ta shafi kafa masarautun zuwa lokacin da za ta saurari karar da ke gabanta.

Sai dai gwamnatin jihar Kanon ba ta bi umarnin ba, don ba ta karbi wani sako mai kamar hakan ba, sai dai kawai ta ga ana yada wa a shafukan sada zumunta.

Tun a ranar Lahadi gwamna Ganduje ya mika wa sarakunan sanda, amma a wata masarautar sai cikin dare aka yi bikin.

Gwamnatin Kano ta ce a shafukan sada zumunta kawai ta ji batun da ake yadawa game da umarnin babbar kotu, wanda kuma a cewarta bai isa hujja ba.

kanoHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES

Sai dai Barista Maryam ta ce idan har kotu ta bayar da irin wannan umarni wanda ba lallai ya kasance hannu da hannu ba – yana iya zama ta hannun wani ko ta jaridu da ma kafafan sada zumunta – ya zama wajibi a mutunta umarninta.

”In dai kotu ta bayar da umarni har aka wallafata to ya zama dole doka ta yi aikinta, kuma a bi umarninta ba lallai wai sai hannu da hannu ba.”

Lauyar ta kuma ce duk wanda aka samu da yin gaban kansa to laifi ne mai zaman kansa, kuma ana iya kai mutum kotu a hukunta shi a kan hakan.

Yadda aka raba masarautun Kano
Image captionYadda aka raba masarautun Kano

Masana shari’a dai na ganin cewa an yi gaggawa wajen aiwatar da wannan doka, ganin yadda komai cikin sa’o’i 72 aka aiwatar.

”A sani na wannan shi ne karon farko da kudirin doka ya tsallake karatun farko da na biyu da uku har aka sa mata hannu a cikin kankanin lokaci,” in ji Barrista Maryam

Har yanzu dai takaddama ba ta kare ba kan wannan nadin, inda wasu ke ganin a matsayin bi-ta-da-kulli saboda takun-sakar da ake zargin ya wanzu tsakanin sarki Muhammadu Sunusi na II da gwamnati, batun da Gwamna Ganduje ya musanta

Author

ilh5qdbyak81@n3plcpnl0159.prod.ams3.secureserver.net

Leave a Reply

Your email address will not be published.