0 Comments

Hausa ➕  ta tabbatar da labarin da ke cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari garin Daura a jihar Katsina – wato mahaifar Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a ranar Laraba.

Shugaban karamar hukumar Daura na riko Injiniya Abba Mato ya shaida wa Hausa ➕  cewa bayan sallar magriba ne maharan suka kai wa garin farmaki.

Ya kuma ce sun sace surukin dogarin Shugaba Buhari, wato Magajin Garin Daura, Alhaji Musa Umar.

“Bayan shi da suka tafi da shi, maharan wadanda suka zo a mota daya, ba su harbi ko taba kowa ba,” in ji Abba Mato.

Daga nan, ya ce jami’an tsaro sun dukufa aikinsu don ganin an kubutar da shi daga hannun maharan.

Sai dai zuwa yanzu fadar shugaban kasar ba ta ce komai ba kan wannan batun.

Har wa yau, a ranar Laraba ne aka yi jana’izar mutum 14, wadanda suka mutu sanadiyyar wani harin da wasu mahara suka kai karamar hukumar Safana shi ma a jihar ta Katsina.

Dan majalisar dokokin yankin a majalisar jihar Katsina, Honorabul Abduljalal Haruna Runka, ya shaida wa Hausa ➕ cewa maharan sun kai farmaki ne a kauyen Gobirawa da kuma Shaka Fito.

Kazalika dan majalisar ya ce maharan sun sace mata da wasu daga yankin karamar hukumar.

Author

ilh5qdbyak81@n3plcpnl0159.prod.ams3.secureserver.net

Leave a Reply

Your email address will not be published.