0 Comments

Najeriya ta lashe gasar cin kofin kwallon kafa ta mata ta 2018 da aka yi ranar Asabar bayan ta doke kasar Afrika ta kudu da ci 4-3 a bugun fanality a wasan karshen da suka yi a birnin Accra.

Kasashen biyu sun tashi canjaras bayan da suka yi minituna 120 suna wasa , inda mai tsaron gidan Najeriya Tochukwu Oluehi ta kare kwalon Linda Motihalo ta Afrika ta kudu shiga cikin raga.

Tun farko yar wasan tsakiya Asisat Oshoala ta baras ta kwallo a wasan fenality .

Tawagar kwallon kafa ta Super Falcons, wadda ta je Ghana dominta kare kabunta ta , ta sake nuna cewa ruwa ba sa’ar kwando bane a gasar cin kofin kallon kafa ta mata , nda za ta dauki kofi a karo na 9 .

Da farko bangarorin biyu sun rika kokarin ganin cewa sun sha gaban juna .

Yan wasan Afrika ta kudu sun rika kai kwallo gidan Najeriya ko da yake yan wasan baya sun dakile hare haren da aka rika kai mu su.

Rita Chikwelu kyaftin din NajeriyaHakkin mallakar hotoBBC SPORT
Image captionKyaftin din Najeriya Rita Chikwelu rike da kofin

Sai dai bayan mintuna 20 da wasa, yan wasan Najeriya suka farga , inda Asisat Oshaola ta kasa saka kwallon da Ngozi Okobi ta buga mata

Yadda wasan fenality ya kasance

Da farko yan wasan Najeriya sun fara buga wasan fenality ne ba tare da samun nasara ba inda kwallon da Onome Ebi ta buga be shiga raga ba sai dai Noko Matlou ta yi nasara zira kwallo a cikin ragar tawagar Banyana Banyana.

Ngozi Ebere ta sake zira kwallo a cikin raga ya yin da Lebohang Ramalepe ta Afrika ta kudu.

Rita Chikwelu ta sa Najeriya a gaba da ci 2-1 sai dai Mpumi Nyandeni ta maida martani .

Chinwendu Ihezuo ta sake sa Najeriya a gaba da ci 3-2 , ya yin da Mamello Makhabane ita ma ta saka kwallo a cikin ragar Najeriya .

Chinaza Love Uchendu ta sa Najeriya a gaba da ci 4-3 sai dai mai tsaron gidan Najeriya ta kare kwallon Motlhalo,abinda ya ba yan Najeriya damar samun nasara .

Author

ilh5qdbyak81@n3plcpnl0159.prod.ams3.secureserver.net

Leave a Reply

Your email address will not be published.