0 Comments

Jami’an ‘yan sanda masu farin kaya a Najeriya wato DSS a jihar Kaduna sun ce sun kama mutane shida da suke zargi da halaka basaraken nan na jihar Kaduna, Agwan Adara Dokta Maiwada Galadima.

Jami’an na DSS dai sun bayyana cewa mutane 22 suke nema bisa zargin halaka Dokta Maiwada Galadima bayan sun karbi kudin fansa.

Sacewa da kuma halaka basaraken dai ya kara rura wutar rikicin addini da kabilanci a jihar Kaduna, rikicin da ya haifar da asarar rayuka.

A wajen wani taron manema labarai, da hukumar DSS a jihar Kaduna ta gudanar ranar Laraba, daraktan hukumar Malam Mahmud Ningi ya ce sun kama mutum shida.

Ya ce a cikin wadanda aka kama din har da wanda ke zargi da jagorantar mutanen da suka sace da kuma kashe Agwan Adaran.

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce ta yi farin ciki da kama mutanen da aka yi.

Kakakin gwamnatin ta Kaduna, Samuel Aruwan, ya ce gwamnati ta dukufa wajen ganin an hukunta duk wanda aka samu da hannu a kisan basaraken.

 

Author

ilh5qdbyak81@n3plcpnl0159.prod.ams3.secureserver.net

Leave a Reply

Your email address will not be published.