0 Comments

Sanarwar da rundunar ta wallafa shafinta na Twitter ta kara da cewa Laftanar Janar Buratai ba ya cikin motar lokacin da ta yi hatsari.

“Motar aiki ta babban hafsan rundunar sojin kasa ta yi hatsari a garin Jere a kan hanyarta ta zuwa Kaduna ranar 11 ga watan Nuwamban 2018 da misalin karfe 6.00 na yamma. Motar na cikin ayarin motoci lokacin da wata mota ta kauce daga kan hanyarta ta doki tasa,” in ji sanarwar.

Rundunar sojin ta ce mai tsaron lafiyar babban hafsan rundunar sojin ya samu raunuka inda aka dauke shi zuwa wani asibiti da ke kusa.

Daga bisani rundunar sojin ta ce an kai mai tsaron lafiyar Janar Buratai wani asibitin soji domin kula da lafiyarsa.

Kazalika an sanar da ‘yan sanda faruwar lamarin inda aka soma bincike.

Sojojin sun ce binciken farko ya nuna cewa direban motar da ya bugi ta Laftanar Janar Buratai ya sha barasa gabanin ya soma tuki.

Sojoji sun ce direban motar da ya bugi motar Buratai sha barasa gabanin ya soma tuki

Author

ilh5qdbyak81@n3plcpnl0159.prod.ams3.secureserver.net

Leave a Reply

Your email address will not be published.