0 Comments

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada Mele Kolo Kyari a matsayin sabon shugaban kamfanin mai na kasar, NNPC.

Wata sanarwa da mai magana da yawun kamfanin, Ndu Ughamadu, ta fitar ta ce Shugaba Buhari ya nada wasu sabbin shugabannin bangarorin kamfanin guda bakwai.

Har ya zuwa lokacin da aka nada shi sabon shugaban, Mele Kyari shi shugaban banagaren harkokin danyen mai na kamfanin, kuma tun watan Mayun 2018, shi ne wakilin Najeriya a Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur wato OPEC.

Shugaba Buhari ya bayar da umarnin cewa sabon shugaban da sabbin shugabannin bangarorin za su yi aiki ne tare da masu rike da mukamin na da har sai ranar 7 ga watan Yulin 2019, don tabbatar da cewa an mika aikin ba tare da wata tangarda ba.

A ranar 8 ga watan Yulin 2019 ne dai sabbin shugabannin za su fara aiki.

Shugabannin bangarorin da aka nada dai sun hada da Mista Roland Ewubare a matsayin shugaban bangaren hako danyen man fetur da Mustapha Yunusa Yakubu shugaban bangaren tacewa da abubuwan da ake samarwa bayan tacewa.

Yusuf Usman shi ne sabon shugaban iskar gas da makamashi, sai Lawrencia Nwadiabuwa Ndupu shugabar bangaren kasuwanci.

An kuma nada Umar Isa Ajiya a matsayin babban jami’in kula da harkokin kudi, da Adeyemi Adetunji shugaban bangaren tacewa da siyarwa.

Sai Farouk Garba Sa’id shugaban bangaren harkokin ayyukan kamfanin.

Mista Ughamadu ya ce tsohon shugaban kamfanin Maikanti Baru ya taya sabbin shugabannin murna.

Wane ne sabon Shugaban NNPC?

  • An haifi Mele Kyari ran 8 ga watan Janairun 1965 a Maiduguri, jihar Barno
  • Ya yi makarantar sakandare a Government Community Secondary School da ke Biu a jihar Borno daga shekarar 1977 zuwa ta 1982
  • Mista Kyari ya kammala digirinsa a Jami’ar Maiduguri a 1987 a fannin ilimin binciken karkashin kasa
  • Shi ne wakilin Najeriya a Kungiyar kasashe masu arzikin manfetur, OPEC kafin nada shi shugaban NNPC
  • Sabon shugaban ba shi da dangantaka da Shugaban Ma’aikatan Shugaba Buhari, Abba Kyari
  • A shekarar 2007, Kyari ya ci kyautar shugaban NNPC ta Ma’aikacin da ya fi ko wanne kwazo
  • A shekarar 2007, an ba shi kyautar GED CS ta kwazo a fannin shugabanci
  • Kyari ya jagoranci wata tawaga da ta tafi da harkokin sayar da abubuwan da ake sayarwa bayan tace mai daga 2016 zuwan yanzu, abin kuma da ya ja Najeriya ta adana dala miliyan daya a shekarar 2016
  • Kyari mamba ne a kungiyar kwadago, kuma babu mamaki shi ya sa abokan aikinsa ‘yan kungiyoyin kwadago ke kiransa “Grand Chairman”, wato babban ciyaman.

Author

ilh5qdbyak81@n3plcpnl0159.prod.ams3.secureserver.net

Leave a Reply

Your email address will not be published.