0 Comments

Mista Kanu ya ce kungiyar leken asiri ta Isra’ila tana taimakonsa

Gwamnatin Najeriya ta mayar da martani kan wani hoton bidiyo da ake yada wa a kafofin sada zumunta dauke da muryar wani wanda yake ikirarin shi ne Nnamdi Kanu, jagoran kungiyar IPOB inda a ciki yake cewa zai dawo kasar.

Gwamnatin ta ce, idan har da gaske ne jagoran ‘yan kungiyar IPOB da ke fafutikar kafa kasar Biafra ya yi bayani a bidiyon, “to gaskiya ta fara bayyana game da zargin da ake yi mata na salwantar da shi, kuma tana dakon shigarsa kasar.”

A bangare guda kuma babu ma tabbas kan lokacin da aka dauki hotunan Kanu da ake ta yadawa cewa ya bayyana a Isra’ila.

Mai magana da yawun shugaban Najeriyar Malam Garba Shehu, ya shaida wa BBC Hausa cewa: ” In har hoton bidiyon da ya nuna Nnamdi Kanu na magana toh gaskiya ta fito a kan zargin da ake wa gwamnati cewa ta salwantar da shi”.

Ya ce gwamnatin Najeriya ta shiga cikin tsaka mai wuya kan zargin da ake mata kan ta kashe ko ta salwantar da Nnamdi Kanu.
Tun yaushe aka daina jin duriyar Nnamdi Kanu?

Mista Kanu mutum mai yawan jawo ce-ce-ku-ce kuma shugaban ‘yan kungiyar IPOB ya bace a shekarar da ta gabata bayan magoya bayansa da kuma sojoji sun yi rikici a jihar Abia.

Yawancin magoya bayan kungiyar IPOB sun zargi sojojin da kashe shugabansu.

An dage shari’ar da ake tuhumarsa da cin amanar kasa saboda rashin bayyanarsa a kotu, inda lauyansa ya ce sojoji sun kai wa iyalinsa hari lokacin da suke aiki, daga nan suka kashe shi ko kuma sace shi.

Jagoran kungiyar ‘yan IPOB din ya bayyana ne a wani hoton bidiyo ranar Juma’a; yayin da lauyansa Ifeanyi Ejiofor ya bayyana cewa ya jima da yin magana da shi.

Sai dai kuma hoton bidiyon ya nuna Mista Kanu a kasar Isra’ila, amma kuma gwamnatin kasar ta ce Mista Kanu bai shiga kasar ba, “sai dai idan bidiyon tsohon ne.”

Ranar Lahadi Mista Knau ya yanke shawarar wallafa wani bayani daga inda yake buya.

“Zan dawo da karfina kuma ko sama da kasa za ta hade sai na dawo da Biafra,” in ji Mista Kanu a wani shirin rediyo da aka gani a shafin ‘yan kungiyar IPOB na Facebook.

Ya kuma bukaci ‘yan kungiyarsa da su nemi gudanar da zaben jin ra’ayin jama’a “kan ko suna son ci gaba da zama ‘yan Najeriya ko kuma suna son samun kasar Biafra.”

Buhari Ya Mayar Wa Nnamdi Kanu Martani

 Ku Dakko Android App Dinmu Domin Saukin Dakko Waka Da Bidiyo

 0 146

– Advertisement –

Wane ne Nnamdi Kanu?

Mista Kanu, wanda ke da izinin zama dan kasa na Najeriya da Birtaniya, ya kirkiri kungiyar People Of Biafra (Ipob), a shakarar 2014 domin neman kafa kasar Biafra.

“Idan akwai wani bangare na Najeriya da ke son shiga yankin na Biafra, to muna musu maraba, matukar sun yi amanna da karantarwar addinan Yahudu da Kiristanci…tsarin karantarwar da kasar Biafra ta ginu a kansa.

Shirin samar da kasar Biafra dai ba sabon abu ba ne.

A shekarar 1967 shugabannin kabilar Igbo sun ayyana kasar Biafra, bayan wani mummunan yakin basasa, wanda ya jawo mutuwar kusan mutum miliyan daya, amma an samu galaba a kan masu neman ballewar.

Mista Kanu shi ne na baya-bayan nan a kabilar Igbo da ke fafutukar ci gaba da gwagwarmayar neman kafa kasar Biafra.

Biafra a takaice:
Image caption Ipob claims these existing states would make up an independent Biafra

Wani tsohon sojan Najeriya Odumegwu-Ojukwu ne ya fara ayyana jamhuriya ta farko ta neman kafa kasar Biafra a shekarar 1967
Ya jagoranci dakarun sojin da mafi yawansu ‘yan kabilar Igbo ne a wani yakin basasa mai muni da aka shafe shekara uku ana yi, ya kuma zo karshe a 1970
Fiye da mutum miliyan daya ne suka rasa rayukansu, mafi yawansu saboda yunwa
Bayan gomman shekaru da kawo karshen rikiicin Biafra da sojoji suka yi, sai kuma kungiyoyin ‘yan aware suka dinga jan hankulan matasa domin goyon bayan akidar
Suna jin cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ba ta damuwa da yankin
Amma gwamnati ta ce korafinsu bai shafi kudu maso arewa ba.

Alaka da Isra’ila

A jawabin da ya gabatar ranar Lahadi, Mista Kanu ya ce har yanzu yana kokarin ganin an kada kuri’ar raba gardama domin yankin kudu maso gabas ya samu damar ballewa daga Najeriya.

Ya nemi magoya bayansa da su kaurace wa zaben da za a gudanar a Najeriya a 2019, har sai gwamnati ta yarda da batun kuri’ar raba gardama.

“Ipob za ta samar da kasar Biafra kuma ba za mu yi zabe ba har sai mun samu an yi kuri’ar raba gardama, ba ma bukatar sasantawa, za mu yi duk abin da za mu iya don tabbatar da hakan,” a cewar Mista Kanu.

“Kwanan nan zan dawo yankin Biafra, kuma sama da kasa za ta hade,” in ji shi.

“Isra’ila ce ta tserar da ni,” ya kara da cewa hukumar leken asirin kasar Mossad na matukar taimaka masa, ba tare da yin karin bayani kan yadda taimakon ya kasance ba.

Har yanzu dai ba a san ta yadda Mista Kanu ya je Isra’ila ba, saboda sanin yadda aka karbi fasfunansa na Najeriya da Birtaniya bayan da aka kama shi.

Author

ilh5qdbyak81@n3plcpnl0159.prod.ams3.secureserver.net

Leave a Reply

Your email address will not be published.