Masu garkuwa da mutane a jihar Zamfara sun sako ‘yan matan nan tagwaye da suka sace a watan jiya.

Dangin tagwayen da kuma wani babban jami’i a Karamar Hukumar Zurmi daga inda aka dauke su, sun tabbatar wa HausaPlus da sakin nasu.

Kuma sun ce suna cikin koshin lafiya.

Sai dai kuma sun ce ba a sako yayarsu ba – wacce aka kama su tare a wani gida da ke garin Dauran a watan jiya a yayin da suka je rabon katin bikin aurensu.

Karin bayani game da Zamfara:

taswirar zamfara

Madogara: Shafin alkalumma na Najeriya.

Total Share 0 Email0Facebook0Twitter0Google plus0