0 Comments

Rundunar ‘yan sanda a jihar Plateau da ke Najeriya, ta ce ta kama wasu mutum 19 da ake zargi da hannu a kisan Manjo Janar Alkali mai ritaya.

A wajen wani taron manema labarai da rundunar ta gudanar a Plateau a ranar Lahadin da ta wuce, jami’in hulda da jama’a na rundunar DSP Tyopev Matthias Terna, ya bayyana cewa sakamakon binciken da aka gudanar a kan wadanda ke da hannu a kisan marigayin, yanzu rundunar ta kama mutunen da ake zargin.

Dama dai tun a watan da ya gabata sojoji sun mika wa rundunar ‘yan sandan mutum 13 da ake zargi da hannu a kisan sojan domin gudanar da bincike a kansu.

Bayan zurfafa bincike ne rundunar ta tabbatar da karin wasu mutum takwas da ake nema ruwa a jallo a kan zargin kisan.

Mutanen da sojojin suka mikawa rundunar ‘yan sandan su 13 da kuma wadanda rundunar ta kama da kanta da ma wadanda ta ke nema ruwa a jallo sun hadar da Pam Chuwang Kim, wanda ke da masaniya a kan lamarin, sai Michael James, wanda shi kuma mazaunin kauyen da abin ya faru ne, ma’ana ya ga lokacin da aka kashe Janar din, kuma ya san wadanda suka yi kisan amma ya yi shiru har sai da aka kama shi.

Sauran sun hadar da Dung Pam, wanda aka kama shi sakamakon mallakar makamai ciki har da bindiga, sai Rebecca Gyang Pam, wadda ita ma mazauniyar kauyen da abin ya faru ce, kuma tana daya daga cikin matan da suka hakikance cewa ba za a duba ko haka rijiyar da aka gano gawar Janar Alkali ba.

Shi kuwa Stanley Onuchukwu an kama shi ne saboda yana da wani gidan bulo da ke kusa da rijiyar da aka gano gawar Janar din, kuma ya samu labarin cewa an tura motar janar din cikin ruwa daga ma’aikatansa amma kuma ya gaza bayar da bayanai ya yi shiru da bakinsa, da dai sauran mutanen da sojojin suka kama bisa zargin hannusu a kisan.

Har yanzu dai ana ci gaba da kokarin gano sauran mutum biyun da ake zargi da hannu a kisan Janar din.

Wannan layi ne

A ranar Laraba ne rundunar sojin Najeriya ta sanar da cewa ta kama mutum 30 a yankin Doi Du na jihar Filato a kokarinta na neman Manjo Janar IM Alkali, wanda ya bace tun watan da ya gabata.

Tun a watan Satumba ne iyalan Janar Alkali suka sanar da labarin bacewarsa, inda suka ce ya bar gidansa da ke Abuja a ranar 3 ga watan don zuwa Bauchi inda yake da gona, amma tun daga sannan ba a ji duriyarsa ba, kuma wayoyinsa ba sa tafiya.

Ana zargin cewa an sace Janar Alkali ne wanda yake yin bulaguron a motarsa.

A ranar 29 ga watan Satumba ne kuma rundunar cika aiki da babban hafsan sojin kasa ta Najeriya Laftanal Janar Tukur Buratai ya kafa don neman Janar Alkali, ta gano motarsa a wani kududdufi da ke Lafendeg a yankin Du na karamar hukumar Jos Ta Kudu.

An yi jana’izar Janar Idris Alkali mai ritaya a Abuja, babban birnin Najeriya a ranar Asabar din da ta wuce.

Mutane da dama ne ciki har da babban hafsan sojin kasa na Najeriya Janar Yusuf Buratai, ne suka halarci jana’izar Janar din.

 

Author

ilh5qdbyak81@n3plcpnl0159.prod.ams3.secureserver.net

Leave a Reply

Your email address will not be published.