0 Comments

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayar da takardar kama aiki ga sabbin sarkunan jihar Kano da aka kirkira.

An gudanar da taron ne dai a babban dakin taro da ke filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata a Kano.

Sai dai wani abin mamaki shi ne a baya an saba ganin idan an zo taro irin wannan, gwamna kan mika takardar kama aiki ga sarakuna a bainar jama’a amma sai dai rahotanni na cewar an tura masu takardunsu ne gidajen su tun a daren Juma’a.

Sarakunan da aka bai wa takardun sun hada da Alhaji Aminu Ado Bayero wanda shi zai jagoranci masarautar Bichi, da kuma Dakta Ibrahim Abubakar a matsayin sarkin Karaye sai Tafida Abubakar Ila a matsayin sarkin Rano da kuma Alhaji Ibrahim Abdulkadir a matsayin sarkin Gaya.

Bayar da takardun na zuwa ne kwana daya bayan da wata kotun jihar ta ba da umarnin cewa gwamnati da majalisar dokokin jihar su dakatar da duk wani mataki na kirkirar sabbin masarautu a jihar ta Kano har sai ta saurari karar da wasu ‘yan majalisa suka shigar gabanta suna kalubalantar matakin yin dokar.

Sai dai a na ta bangaren, gwamnatin jihar ta ce ita bata ga wata takardar kotu ba a hukumance da ta ce ta dakatar da kirkira ko kuma bayar da takardar kama aiki ga sabbin sarakunan ba.

BBC

A wajen taron, gwamnan ya bayyana cewa dalilin kirkiro masarautun shi ne hada kan al’umma da samar da tsaro da kuma kawo ci gaba ga jihar ta Kano.

Dukkanin sabbin sarakunan sun yi jawabin godiya ga gwamnan inda kuma suka tabbatar da cewa za su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Sai dai Sarkin na Kano Muhammadu Sanusi II bai hallarci wannan taro ba kuma har yanzu bai ce komai dangane da sauya fasali da kuma kirkirar sabbin masarautun da aka yi a jihar ta Kano ba.

Wasu na ganin cewa an yi haka ne domin rage karfin ikon Muhammadu Sanusi II sakamakon irin suka da ya ke yi ga tsare-tsaren gwamnati da kuma zargin katsalandan a harkokin siyasa.

Wasu daga cikin ra’ayoyin jama’a kan sabbin masarautun Kano

Author

ilh5qdbyak81@n3plcpnl0159.prod.ams3.secureserver.net

Leave a Reply

Your email address will not be published.